Jammaje Academy

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Jammaje Academy


Gabatarwa

Jammaje Akadami, wadda kuma ake rubutawa da Jammaje Academy a Turance, fitacciyar makarantar koyar da Turanci zalla ce. Daga baya fukafukanta suka faɗaɗa zuwa koyar da sauran fannonin ilimi ciki kuma har da horas da ƙwararrun ‘yan wasan fim a ɓangarori biyu; Hausa da Ingilishi, abin da ba kasafai ake koyar da shi a makarantun Najeriya ba musamman ma Arewa.

Sha’awar harshen Turanci, ita ce abar da ta zaburantar da matashi mai ƙwazo, Kabiru Musa Jammaje ya fara rubuta wani littafi mai suna Dependable English, daga baya kuma ya sake rubuta wani littafin mai suna New Way of Learning English, littafin da ya sauya fasalin yadda ake rubuta littattafan koyon Turanci da aka fi sani da Koyi da Kanka.

Bayan bayyanar waɗancan littattafai guda biyu a kasuwannin Kano da kewaye, wasu matasa suka kwaɗaitu da koyon wannan harshe na Turanci a hannun wannan sabon marubuci; Kabiru Musa Jammaje, abin da ya saka ya fara karantar da su a ƙofar gida kafin daga baya ya kafa makaranta wadda aka raɗa wa suna Jammaje Evening Classes wadda ita ce ta haɓaka zuwa wannan katafariyar cibiya mai suna Jammaje Academy.

Makarantar ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen haɓɓaka harkar ilimi musamman ta fuskacin ɗora mutane a kan tafarkin fahimtar shi kansa harshen Turancin, samar da guraben ayyukan yi, fitar da sabon salon koyar da harshen Turanci ta radiyo, da sauran muhimman abubuwan cigaba waɗanda ake iya gani da kuma ji a cikin Birnin Kano da ma wasu ƙasashen Afirka da dama.

Fitattun cibiyoyin bayar da horo kan harshen Turanci irin su M.M. Haruna Academy, Kamfa English Centre, Yakasai English Centre, misalai ne na cibiyoyin da Jammaje Academy ta haifa ƙari akan nata rassan waɗanda za a iya gani a muhallin da ya dace a cikin wannan rubutu.

Haka ne, ana iya cewa da wannan cibiya sam-barka! Rumbun Ilimi ya ƙuduri aniyar fayyace muku yadda ta wakana daga farkon kafa ta a shekarar 2002 zuwa yau (2021); tsawon shekaru goma sha tara kenan ta cikin wannan rubutu.

Daga Tushe

“Buƙatar son koyon harshen Turanci daga wajena da jama’a suka yi biyowa bayan rubuta wasu littattafai da na yi; Dependable English da kuma New Way of Learning English waɗanda suke ƙari ne a kan tsananin sha’awar harshen Ingilishi da nake da ita a ƙashin kaina, su ne dalilai guda biyu da suka sabauta kafa wannan makaranta” in ji Alhaji Kabiru Musa Jammaje a lokacin da ya amsa tambayar da na yi masa kan dalilin kafa wannan makaranta a ranar 22 ga watan Satumba na shekarar 2021.

A cikin shekarar 2002 makarantar ta fara koyar da wasu matasa yadda za su riƙa yin karatu da rubutu cikin harshen Turanci. Ana cikin gudanar da wannan darasi wanda kusan na yaƙi da jahilci ne sai aka kafa makarantar da aka raɗawa suna Jammaje Evening Classes tare kuma da yi mata rijista da Hukumar Yaƙi da Jahilci; Agency for Mass Education da ke Kano inda aka samu sahalewar hukumar kan gabatar da darasin da aka fara gudanar da shi a makarantar Firmaren Ɗandago (Ɗandago Primary School) da ke cikin ƙwaryar birnin Kano. Darusan da aka koyar a wannan mataki sun haɗa da Ingilishi, lissafi, health science da kuma social studies.

Kabiru Musa Jammaje, Muhammadu Warure daga baya kuma Abba Habib wanda daga baya ya zama ma’aikacin gidan talabijin na Jahar Kano (Abubakar Rimi Radio and Television), su ne malaman wannan makaranta na farko. Sai kuma ɗalibin malami, Salisu Mahdi wanda yanzu yake ma’akaci ne a hukumar lafiya ta jahar Kano da shima ya zama malami bayan kammala ɗaukar darasi a makarantar.

A shekarar 2005, biyowa bayan bunƙasar makarantar da karɓuwar waɗancan littattafai da suka zama sanadin kafuwarta suka haifar da wata sabuwar buƙatar ta faɗaɗa hanyoyin karantarwa. Wannan dalili ya saka aka canjawa wannan makaranta suna daga Jammaje Evening Classes zuwa Jammaje English Club wanda aka riƙa rubuta shi a taƙaice da JEC.

Samun wannan sabon suna ya haifar da cikakkiyar damar mayar da hankali kan karantar da harshen Turanci zalla ta hanyar samar da wasu sababbin shirye-shirye da kuma rage sauran darusan zuwa ƙwaya ɗaya rak!

Ƙungiyar Marubuta mai suna Optimum Writers Association (OWA), wadda daga baya aka canja mata suna zuwa Association of Fiction and None-Fiction Writers (AFINOW); gabatar da shirin koyar da Turanci mai suna Creative Writers cikin harshen Hausa a gidan radiyon Freedom da ke Kano, daga baya kuma a rassansa da ke Dutsen Jahar Jigawa da kuma Kaduna; gudanar da taron gabatar da takardun wata-wata mai suna Monthly Writer Forum, domin gogar da matasa a fagen rubutun Turanci da Hausa; bin unguwannin ciki da wajen birnin Kano ana gabatar da jawabai kan muhimmanci ilimi da kuma harshen Ingilishi suna daga cikin sababbin shirye-shiryen da JEC ta zo da su.

Bayan shekaru biyu cur; 2005 zuwa 2007 ana gudanar da waɗannan darusa da sauran karatuttuka sai takunkumi ya fi ƙarfin bakin kaza; wato ajujuwan da aka sahalewa wannan cibiyar domin gudanar da karatuttukanta a wannan makarantar firmare ta Ɗandago suka yi mata kaɗan. Saboda haka canjin sheƙa ya zama dole, wannan cibiya ta tashi daga Firamaren Ɗandago ta koma Aminu Kano Commercial College (AKCC) da ke Gwauron Dutse.

A shekarar 2009 aka sake canja wa wannan cibiya suna da kuma fasalin gudanar da karatuttuka. Sunanta ya tashi daga Jammaje English Club zuwa Jammaje English Centre.

A ƙarƙashin sabon fasalin gudanar da karatuttukan wannan cibiya ne aka samu halatar shehinan malaman Turanci domin karantarwa a wannan cibiya. Maluman guda biyu daga Tsangayar Koyar da Harshen Turanci ta Jami’ar Bayero da ke Kano su ne Farfesa Ibrahim Bello Kano da kuma Farfesa Mustafa Ahmad Isa wanda daga baya ya zama Mataimakin Shugaban Jami’ar North-West na farko wanda ita ma yanzu aka canja mata suna zuwa Maitama Sule University domin martaba suna da kuma tsawaita ambaton marigayi Maigirma Ɗanmasanin Kano, Alhaji Yusuf Mataima Sule.

A cikin shekarar 2013, aka sake canja wa wannan makaranta suna biyowa bayan buƙatar da ake da ita ta sake faɗaɗa darrusan da za a riƙa koyarwa a wannan makaranta.

Wannan kuma, ya biyo bayan tsawon shekaru da wannan cibiya ta ɗauka tana gudanar da shirye-shriyen koyar da Turanci a tashoshin Gidan Radiyon Freedom da ke Kano, Dutse da kuma Kaduna sai kuma abin da ya ƙaru na shiga harkar shirya fina-finai da makarantar ta yi. Bisa waɗannan dalilai sai ta tashi daga sunanta na Jammaje English Centre zuwa Jammaje Academy abin da ya bata damar buɗe sababbin darrusa da fagagen samun horo waɗanda daga ciki akwai horas da jaruman fina-finai cikin harshen Hausa da Ingilishi. Wannan suna shi ne sunan da wannan cibiya take amsawa har zuwa yau ɗin nan 2021.

Gudunmawa

Madalla da wannan cibiya ta Jammaje Academy. Cikin waɗannan shekaru goma sha tara (2002 – 2021), wannan cibiya ta samu damar amfanar da al’ummar jahar Kano a matakin farko, Arewancin Najeriya a mataki na biyu, Najeriya a mataki na uku, Afirka a mataki na huɗu da kuma wasu sassan duniya a mataki na ƙarshe.

Wannan cibiya ta Jammaje ta bayar da gudunmawa mai gwaɓi a fannoni rayuwa musamman fannin ilimi da samar da guraben ayyukan yi waɗanda ka iya kasancewa kai tsaye ko kuma a fakaice:

  • Fannin Ilimi: Ta hanyar karantarwar kai tsaye a aji, shirye-shiryen gidajen radiyo, shirya fina-finai, gudanar da tarurrukan ƙarawa juna sani da sauransu, cibiyar ta bayar da gudunmawa wajen ƙara wayar da kan jama’a, yaƙar jahilci, faɗaɗa ilimi ga waɗanda suke da shi a baya da sauransu.
  • Gudanar da Shirye-Shiryen Koyar da Turanci ta Gidajen Radio: A kan wannan gaɓar, Allah ne kaɗai zai iya iyakance dubunai ko miliyoyin al’ummar da suka amfana da wannan tunani na wannan cibiya ta Jammaje da Kabiru Musa Jammaje ya kafa.
    Tun cikin shekarar 2005 ake gudanar da wancan shiri mai suna Creative Writers farko a gidan radiyon Freedom da ke Kano daga baya kuma a rassanta na Dutse babban birnin Jahar Jigawa da kuma Kaduna babban birnin Jahar Kaduna. Daga baya a cikin shekarar 2020 shirin ya samu canjin sheƙa da kuma suna daga Freedom zuwa Vision FM da ke Kano wanda aka laƙabawa suna Book Time shirin da har yau shi Kabiru Musa Jammaje yake gudanar da shi da kansa. Kenan, yau shekaru goma sha shid cur ana karantar da al’ummar da Allah ne kaɗai zai iya iyakance su ta cikin wannan shiri.
    English for Learners, shirin koyar da Turanci da Anas Kanfa ke gabatarwa a gidan radiyon Rahama da ke Kano; Express English, shirin koyar da Turanci da M. M. Haruna ke gabatarwa a gidan radiyon Express da ke Kano da kuma Mind Your English, shima shirin koyar da Turanci da Abba Idris Musa ke gabatarwa a gidan radiyon Guaranty da ke Kano duka ‘ya’ya ne na wannan cibiya mai albarka.
  • Guraben Samar da Ayyukan yi: Samuwar Jammaje Academy tun daga tushe, ya samar da kafuwar fitattun makarantu irinta, samuwar gogaggun ‘yan jaridar da ake damawa da su a fitattun kafafen yaɗa labaru, fitattun mawaƙan Hausa, gogaggun jaruman fina-finan Hausa da sauransu. Kaɗan daga cikin irin waɗannan mutane akwai:
    1. Muzammil Ibrahim Yakasai shugaban cibiyar Yakasai English Centre sannan kuma gogaggen ɗanjarida wanda ke aiki a gidan radiyon Dala da ke Kano.
    2. M. M. Haruna shugaban cibiyar M. M. Haruna English Academy sannan kuma mai gabatar da shirin koyar da Ingilishi a gidan radiyon Express da ke Kano.
    3. Anas Kanfa, shugaban cibiyar Kanfa English Centre sannan kuma mai gabatar da shirin koyar da Ingilishi a gidan radiyon Rahama da ke Kanon Dabo.
    4. Mu’azu Musa Ibrahim wanda ke gabatar da fitattun shirye-shiryen yara a gidan radiyon Dala da ke Kano.
    5. Falalu A Ɗorayi wanda yake fitaccen mashiryin fina-finan Hausa ne.
    6. Bello Ibrahim Billy O wanda fitacce ne shi a fagen waƙar fina-finan Hausa da sauransu.
    7. Zahra Musa da ita kuma ta kasance fitacciyar ‘yar jarida a gidan radiyon Vision da ke Kano.
    8. Nuhu Abdullahi fitaccen jarumi ne shi a duniyar fina-finan Hausa.
    9. Basiru Shu’aibu Jammaje wanda ya zama fitaccen marubucin littattafan Turaci da Hausa.
    10. Rabi’u Shamma wanda shi kuma fitaccen ɗan fafutikar ‘yancin bil’adama ne.

Wasu daga cikin waɗannan sunaye da aka ambata a sama, sun kafa cibiyoyin da suma suka samar da guraben ayyukan yi na kai tsaye tare kuma da cigaba da faɗaɗa waccar manufa ta ilimantarwa da wayar da kan al’umma. M.M. Haruna English Academy, Yakasai English Centre da Kanfa English Centre cikakkun misalai ne.

Rassa

Daga kafa wannan cibiya a cikin shekarar 2002 zuwa yau 2021, tana da rassa a wasu daga cikin biranen Najeriya ciki kuma har da babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja, Kaduna, Dutse, Katsina, Sakkwato, Zariya, Gombe da kuma ƙarin cibiya ɗaya a unguwar Tarauni da ke cikin Kanon Dabo.

Kwasa-Kwasai

Tsari da kuma salon kwasan-kwasan da wannan cibiya take gudanarwa ingancinsu ya kai. Ga yadda kwasa-kwasan suke:

  1. Turanci Zalla: Kwas ne da ke gogar da dukkan wanda ya halarce shi zuwa matakin ƙwarewa a fannin hulɗa da harshen Turanci ta kowace fuska. An kasa wannan kwas zuwa matakai uku kamar haka:
    • Matakin Farko, abin da a Turance aka kira Basic. Mataki ne da ake farawa da shi. A wannan mataki ake koyar da ɗalibi karantawa, rubutawa, sauraro da kuma yin magana cikin harshen Turanci.
    • Matsakaicin Mataki, abin da a Turance aka kira Intermediate Level. A wannan mataki ake ƙara goggar da ɗalibi kan abubuwan da ya koya a matakin farko tare kuma da sanar da shi ƙa’idojin Turanci; wato nahawun Turanci abin da a Turancen ake kira English Grammar.
    • Babban Aji, abin da aka kira Advance Level a Turance. A wannan mataki ake koyar da ɗalibai abubuwan da suka haɗa da adabin Turanci (English literature), zuzzurfan nahawun Turanci, rubutun jawabin, gabatar da jawabi a bainar jama’a (public speaking), da sauran muhimman darusa.
      A wannan mataki ake gogar da ɗalibi sosai zuwa matakin ƙwarewa ta yadda ana kammalawa an zama kadara da ma’ana ta cewa za a iya cin gashin kai a duk inda ya samu kai.
  2. Gamagari, da ma’ana ta General Knowledge a Turance kenan. Kwas ne da wanda ya halarce shi zai koyi darrusa masu tarin yawa waɗanda ake koyarwa a makarantun Najeriya.
    Manufar samar da wannan kwas ita ce shirya ɗalibi tsaf domin samun damar tunkarar jarabawar da aka faɗi a baya ko kuma shiga makarantar gaba da sikandire a kintse. Kwas ne da aka shirya shi a salon irin na kwas ɗin share fagen shiga jami’a, wato remedial course kenan a Turance.
  3. Kwas Ɗin Zama Jarumi a Fim, wanda aka kira Acting Class a Turance. Kwas ne da ke karantar da ƙwarewa a harkar jarumtakar fim ɗin Hausa da na Inglishi.

Sauran Abubuwa

Ƙari a kan waɗancan kwasa-kwasai da aka lissafa a sama, cibiyar Jammaje tana gudanar da wasu abubuwan da suka haɗa da:

  1. Karantarwa ta Intanet, abin da aka fi sani a Turance da eLearning wanda ake iya shiga ta nan
  2. Wallafa Littattafai.
  3. Shirya Fina-Finai.
  4. Gabatar da Shirye-Shiryen Gidan Radio da sauransu.

Ina da yaƙini ya zuwa wannan gaɓa cewa, mai karatu ya fahimci ta inda aka somo, gurin da ake da kuma gagarumar gudunmawa da wannan cibiya ta Jammaje take bayarwa tare kuma da ɗaukar darrusan da ba za a rasa ba.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub